+ -

عن صالح بن خَوَّاتِ بْنِ جُبَيْرٍ رضي الله عنه عمّن صلَّى مع رسول الله صلى الله عليه وسلم صلاة ذَاتِ الرِّقَاعِ صلاةَ الخوف: أن طائفة صفَّت معه، وطائفة وِجَاهَ الْعَدُوِّ، فصلَّى بالذين معه ركعة، ثم ثبت قائما، وأتموا لأنفسهم، ثم انصرفوا، فصفُّوا وِجَاهَ الْعَدُوِّ، وجاءت الطائفة الأخرى، فصلَّى بهم الركعة التي بقيت، ثم ثبت جالسا، وأتموا لأنفسهم، ثم سلَّم بهم.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Sale Dan Khauwat Dan Jubair -Allah ya yarda da shi- daga wanda yayi sallar tsoro tare da Annabi a ranar yakin Zaturriqa'a:cewa: wani yanki suka yi sahu tare da Annabi, wani bangaren ya fuskanci abokan gaba,sai ya jagoranci wanda suka yi sahu tare da shi suka sallaci raka'a daya,sannan ya tsaya kyam,su kuma suka cika sallar,sannan suka juya suka fuskanci abokan gaba,su kuma wadancan suka zo,suka sallaci raka'ar da ta rage,tare da Annabi tsira da amincin Allah-,sai ya zauna,su kuma suka ciko raka'ar da ta rage musu, sai Annabi yayi sallama suma suka yi.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya je wani yaki tare da sahabbansa yawancinsu a kasa suke,sai suka gaji har suka nannada yanki a kafafuwansu, duk da dai ba'a yi yakin ba, musulmi ne suka tsorata abokan gabarsu, to a wannan hadisin abokan gab a ba'a bangaren Alkibla suke ba,saboda gidajensu suna gabas da Madina,sai Annabi ya kasa su kashi biyu,wasu suka yi sahu tare da shi,wasu kuma suka fuskanci abokan gaba wadanda masu salla suka juya musu baya,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sallaci raka'a daya tare da sahun farko,sai suka ciko raka'a daya suka yi sallama,sannan suka je suka fuskanci abokan gaba,shi kuma ya tsaya a tsaye, har wadancan masu fuskantar abokan gaba suka zo, ya sallaci raka'ar da ta rage tare da su, sai yayi zamansa suka mike suka ciko raka'a daya,sannan yayi sallama suma suka yi.Jama'ar farko sun dace da samun kabbarar harama tare da liman,ita kuma ta biyu ta dace da samun sallama tare da liman,kuma abokan gaba basu sami dama ba,sahabbai kuma sun samu daidaito wajen samun falalar jam'in.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Portuguese
Manufofin Fassarorin