عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«أَحَبُّ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ مَسَاجِدُهَا، وَأَبْغَضُ الْبِلَادِ إِلَى اللهِ أَسْوَاقُهَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 671]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 671]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi soyuwar gurare a wurin Allah - Mai girma da ɗaukaka - sune masallatan garuruwan; domin su wuraran ayyukan biyayya ga Allah ne, kuma ginshiƙansu akan tsoron Allah ne. Kuma mafi ƙin garuruwa a wajen Allah sune kasuwanninsu; domin cewa galibi guri ne na algus da yaudara da riba da rantse-rantse akan ƙarya, da saɓa alƙawari, da bijirewa ambatan Allah.