عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَنْ عَالَ جَارِيَتَيْنِ حَتَّى تَبْلُغَا جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَنَا وَهُوَ» وَضَمَّ أَصَابِعَهُ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2631]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2631]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda aka azirta shi da 'yan mata biyu ko 'yan uwa mata biyu sai ya tsaya da ɗawainiya da tarbiyya da nusarwa ga alheri da gargaɗarwa daga sharri da makamancin hakan har suka girma suka balaga; zai zo ranar alƙiyama shi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar waɗannan biyun, kuma sai ya haɗa yatsunsa biyu manuniya da na tsakiya.