عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ حَتَّى تُؤْمِنُوا، وَلَا تُؤْمِنُوا حَتَّى تَحَابُّوا، أَوَلَا أَدُلُّكُمْ عَلَى شَيْءٍ إِذَا فَعَلْتُمُوهُ تَحَابَبْتُمْ؟ أَفْشُوا السَّلَامَ بَيْنَكُمْ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 54]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, Ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, , shin ba na shiryar daku akan abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a tsakaninku".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 54]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bayyana cewa ba masu shiga aljanna sai muminai, kuma imani ba ya cika, sannan halin jama'ar musulmai ba ya gyaruwa har sai sashinsu yaso sa shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya shiryar zuwa mafificin al'amuran da su ne soyayya take gamewa, ita ce yada sallama tsakanin musulmai, wacce Allah Ya sanyata gaisuwa ga bayinSa.