عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«السَّاعِي عَلَى الأَرْمَلَةِ وَالمِسْكِينِ، كَالْمُجَاهِدِ فِي سَبِيلِ اللَّهِ، أَوِ القَائِمِ اللَّيْلَ الصَّائِمِ النَّهَارَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5661]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5661]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake tsayuwa akan al’amuran matar da mijinta ya rasu alhali ba ta da wani wanda zai tsaya akan lamuran ta, da kuma miskini mabukaci, yana ciyar dasu yana mai neman lada a wurin Allah - Madaukakin sarki -, to shi a lada kamar mayakine a tafarkin Allah, ko kamar mai tsayuwa ne a sallar tahajjudin da baya gajiya, mai azimin da ba ya hutawa.