عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنين رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ:
جَاءَتْنِي مِسْكِينَةٌ تَحْمِلُ ابْنَتَيْنِ لَهَا، فَأَطْعَمْتُهَا ثَلَاثَ تَمَرَاتٍ، فَأَعْطَتْ كُلَّ وَاحِدَةٍ مِنْهُمَا تَمْرَةً، وَرَفَعَتْ إِلَى فِيهَا تَمْرَةً لِتَأْكُلَهَا، فَاسْتَطْعَمَتْهَا ابْنَتَاهَا، فَشَقَّتِ التَّمْرَةَ الَّتِي كَانَتْ تُرِيدُ أَنْ تَأْكُلَهَا بَيْنَهُمَا، فَأَعْجَبَنِي شَأْنُهَا، فَذَكَرْتُ الَّذِي صَنَعَتْ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «إِنَّ اللهَ قَدْ أَوْجَبَ لَهَا بِهَا الْجَنَّةَ، أَوْ أَعْتَقَهَا بِهَا مِنَ النَّارِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2630]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce :
Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi ƙara ci daga gareta, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci a tsakaninsu, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - abin da ta aikata, sai ya ce: «Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2630]
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ambaci cewa wata mata miskiniya tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu sai ta tambayeta, sai ta bata dabinai uku, sai ta bawa kowacce daga cikin 'ya'yan nata mata biyu dabino ɗaya, kuma ta ɗaga ɗayan zuwa bakinta dan ta ci shi, sai 'ya'yan nata mata biyu suka nemi dabinon da take nufin cinsa, sai ta raba dabinon a tsakaninsu, sai lamarinta ya ƙayatar da Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita -, kuma ta faɗawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abinda matar ta aikata, sai ya ce: Lallai haƙiƙa Allah Ya tabbatar mata aljanna saboda wannan dabinon, ko kuma ya 'yantata daga wuta.