+ -

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسعودٍ رضي الله عنه عن رَسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم قال:
«الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، -ثلاثًا-»، وَمَا مِنَّا إِلَّا، وَلَكِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُذْهِبُهُ بِالتَّوَكُّلِ.

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 3915]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce:
"Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 3915]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga canfi shi ne canfi daga kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, daga tsuntsayene ko dabbobi ko masu larurori ko lambobi ko kwanuka ko makamancin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi a bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya canfa ya kame daga abinda yake nufi. Ya bada labarin cewa hakan shirka ce, kadai canfi ya zama shirka; domin ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah Shi kadai ba shi da abokin tarayya.
Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa wani abu na canfi zai iya darsuwa a zuciyar musulmi, saidai ya wajaba akansa ya tunkude shi da dogaro ga Allah, tare da aikata sabubba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Canfi shirka ne; domin acikinsa akwai rataya zuciya da wanin Allah.
  2. Muhimmancin maimaita mas'aloli muhimmai, dan a kiyaye su kuma su tabbata a cikin zukata.
  3. Dogaro ga Allah - Madaukain sarki - yana tafiyar da canfi.
  4. Umarni da dogaro ga Allah Shi kadai, da rataya zuciya da Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.