عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمنين رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«يُحْشَرُ النَّاسُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ حُفَاةً عُرَاةً غُرْلًا» قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ النِّسَاءُ وَالرِّجَالُ جَمِيعًا يَنْظُرُ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ؟ قَالَ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا عَائِشَةُ، الْأَمْرُ أَشَدُّ مِنْ أَنْ يَنْظُرَ بَعْضُهُمْ إِلَى بَعْضٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2859]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
«Za'a tashi mutane a ranar Lahira marasa takalma tsirara kuma marasa kaciya». Na ce: Ya Manzon Allah! mata da maza baki ɗaya sashinsu yana kallon sashi? Sai (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Ya A'isha, al'amarin ya fi tsanani a ce sashinsu yana kallon sashi».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2859]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta sashin abinda ke cikin ranar alƙiyama, kuma mutane za'a tarasu bayan tashinsu daga ƙaburburansu dan yin hisabi, kuma cewa halinsu zasu zama marasa takalma, tsirara babu tufafi, marasa kaciya kamar ranar da iyayensu suka haifesu, yayin da Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ji hakan sai ta ce tana mai mamaki: Ya Manzon Allah ! maza da mata baki ɗayansu sashinsu yana kallon sashi?! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa: Sha'anin tsayuwar da taruwa bayan tashi daga mutuwa a cikinsa akwai tsorace-tsoracen da zai ɗauke hankalin mutane da idanuwansu daga kallan al'aurori.