+ -

عَن أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيَّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا وُضِعَتِ الجِنَازَةُ وَاحْتَمَلَهَا الرِّجَالُ عَلَى أَعْنَاقِهِمْ فَإِنْ كَانَتْ صَالِحَةً قَالَتْ: قَدِّمُونِي، وَإِنْ كَانَتْ غَيْرَ صَالِحَةٍ قَالَتْ: يَا وَيْلَهَا أَيْنَ يَذْهَبُونَ بِهَا؟ يَسْمَعُ صَوْتَهَا كُلُّ شَيْءٍ إِلَّا الإِنْسَانَ، وَلَوْ سَمِعَهُ صَعِقَ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 1314]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Idan aka ajiye jana'iza (gawa) maza suka ɗauketa akan kafadinsu idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku kaini, idan ba ta gari ba ce kuwa zata ce: Ya kaicanta ina zasu tafi da ita? kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da ace ya ji shi (sautin) da ya suma».

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1314]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan aka ajiye jana'aiza (gawa) akan gado (makara), maza suka ɗauketa akan wuyansu, idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku gabato da ni dan abinda ta gan shi a gabanta na ni'ima, idan ba tagari ba ce zata yi ƙara da sauti abin ƙi: Ya halakarta ina zasu tafi da ita?! dan abinta ta gan shi a gabanta na azaba, kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da a ce ya ji shi da ya suma saboda tsananin abinda ya jishi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mamaci na gari yana ganin abubuwan bushara kafin rufe shi, kafiri kuwa yana kasa haƙuri, kuma yana ganin akasin hakan.
  2. Wasu sautukan wanda ba mutum ba zai ji su, amma mutum ba zai iya jinsu ba.
  3. Sunna ita ce ɗaukar jana'iza (gawa) akan kafadun maza banda mata; saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana mata binta (jana'iza).