عَنْ صَفْوَانَ بْنِ مُحْرِزٍ قَالَ: قَالَ رَجُلٌ لِابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما كَيْفَ سَمِعْتَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: فِي النَّجْوَى؟ قَالَ: سَمِعْتُهُ يَقُولُ:
«يُدْنَى الْمُؤْمِنُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ رَبِّهِ عَزَّ وَجَلَّ، حَتَّى يَضَعَ عَلَيْهِ كَنَفَهُ، فَيُقَرِّرُهُ بِذُنُوبِهِ، فَيَقُولُ: هَلْ تَعْرِفُ؟ فَيَقُولُ: أَيْ رَبِّ أَعْرِفُ، قَالَ: فَإِنِّي قَدْ سَتَرْتُهَا عَلَيْكَ فِي الدُّنْيَا، وَإِنِّي أَغْفِرُهَا لَكَ الْيَوْمَ، فَيُعْطَى صَحِيفَةَ حَسَنَاتِهِ، وَأَمَّا الْكُفَّارُ وَالْمُنَافِقُونَ، فَيُنَادَى بِهِمْ عَلَى رؤُوسِ الْخَلَائِقِ هَؤُلَاءِ الَّذِينَ كَذَبُوا عَلَى اللهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2768]
المزيــد ...
Daga Safwan ɗan Muhriz ya ce: Wani mutum ya ce wa Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - yaya ka ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: A (sha'anin) sirri? ya ce: Na ji shi yana cewa:
"Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa, sai Ya ce: Shin kana sane ? sai ya ce: Eh ya Ubangiji ina sani, ya ce: Lallai cewa Ni haƙiƙa Na suturtasu gareka a duniya, kuma cewa lallai Ni Zan gafarta maka su a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa, amma kafirai da munafukai, sai a kirasu akan kawunan halittu waɗannan sune waɗanda suka yi wa Allah ƙarya".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2768]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da ganawar Allah ga bawanSa mumini ranar alƙiyama, sai ya ce:
Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa sai Ya sanya suturarSa daga ma'abota wurin tsayuwa har ya zama waninsa ba zai yi tsinkaye akan sirrinsa ba, sai ya ce masa:
Shin kana sanin zunubi kaza da kaza... Zai tabbatar masa da zunuban da suke tsakanin bawa da UbangijinSa.
Sai ya ce: Na'am Eh, ya Ubangiji.
Har idan mumini ya firgita ya ji tsoro, sai Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce masa: Lallai cewa Ni na suturta su gareka a duniya, kuma cewa Ni na gafartasu gareka a yau, sai a ba shi takardar kyawawan ayyukansa.
Amma kafiri da munafuki sai a yi kira a gabn mahalarta: Waɗannan sune waɗanda suka yi wa Ubangijinsu ƙarya, ku saurara tsinuwar Allah ta tabbata akan azzalumai.