عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«يُسَلِّمُ الرَّاكِبُ عَلَى المَاشِي، وَالمَاشِي عَلَى القَاعِدِ، وَالقَلِيلُ عَلَى الكَثِيرِ».
وَلِلبُخَارِي: «يُسَلِّمُ الصَّغِيرُ عَلَى الكَبِيرِ، وَالمَارُّ عَلَى القَاعِدِ، وَالقَلِيلُ عَلَى الكَثِيرِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6232]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ke kan abin hawa shi ke sallama ga mai tafiya, mai tafiya kuma yana sallama ga wanda ke zaune, kadan kuma (suna sallama) ga masu yawa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6232]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana shiryarwa ga ladabin yin gaisuwar Musulunci tsakanin mutane "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarsa", Sai karami ya yi sallama ga babba, wanda ke kan abin hawa ga mai tafiya a kasa, mai tafiya a kasa ga wanda ke zaune, adadi kadan ga adadi mai yawa.