عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
أَلَسْتُمْ فِي طَعَامٍ وَشَرَابٍ مَا شِئْتُمْ؟ لَقَدْ رَأَيْتُ نَبِيَّكُمْ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَمَا يَجِدُ مِنَ الدَّقَلِ مَا يَمْلَأُ بِهِ بَطْنَهُ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2977]
المزيــد ...

Daga Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Shin baku kasance kuna yadda kuka so a cikin abin ci da abin sha ba? Haƙiƙa na ga Annabinku - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali bai samu dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi ba.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 2977]

Bayani

Nu'umanu ɗan Bashir - Allah Ya yarda da su - yana ambatawa mutane abinda suke a cikinsa na ni'ima, kuma su basu gushe ba suna yadda suke so a cikin abin cin da abin sha, sannan ya bada labarin halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi bai kasance yana samun dabino mara kyan da zai cika cikinsa da shi saboda yunwa ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin halin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa na gudun duniya.
  2. Kwaɗaitarwa akan gudun duniya da kuma ƙarantuwa daga gareta da kuma koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Tunatar da mutane ni'imomin da suke a cikinsu da kuma kwaɗaitarwa akan godewa Allah a kansu.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (33)