عَنْ الزُّبَيْرِ بْنِ الْعَوَّامِ قَالَ:
لَمَّا نَزَلَتْ: {ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ} [التكاثر: 8]، قَالَ الزُّبَيْرُ: يَا رَسُولَ اللهِ، وَأَيُّ النَّعِيمِ نُسْأَلُ عَنْهُ، وَإِنَّمَا هُمَا الْأَسْوَدَانِ التَّمْرُ وَالْمَاءُ؟ قَالَ: «أَمَا إِنَّهُ سَيَكُونُ».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 3356]
المزيــد ...
Daga Zubairu ɗan Awwam ya ce:
Yayin da (aya) ta sauka {Sannan lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} [Al-Takasur: 8], sai Zubair ya ce: Ya Manzon Allah, shin wace ni'ima ce za a tambayemu game da ita, bakake biyu ba ne kaɗai; dabino da ruwa? sai ya ce: "lallai dai kam daa sannu zai kasance".
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 3356]
Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa!
Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.