Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .
+ -

عَنْ عُبَادَةَ بْنِ الصَّامِتِ رَضيَ اللهُ عنهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«فِي الجَنَّةِ مِائَةُ دَرَجَةٍ مَا بَيْنَ كُلِّ دَرَجَتَيْنِ كَمَا بَيْنَ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، وَالْفِرْدَوْسُ أَعْلاَهَا دَرَجَةً وَمِنْهَا تُفَجَّرُ أَنْهَارُ الجَنَّةِ الأَرْبَعَةُ، وَمِنْ فَوْقِهَا يَكُونُ العَرْشُ، فَإِذَا سَأَلْتُمُ اللَّهَ فَسَلُوهُ الفِرْدَوْسَ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2531]
المزيــد ...

Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».

[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2531]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljannar Lahira akwai darajoji da matsayi ɗari, tsakanin kowace daraja a nisa kamar tsakanin sama da ƙasa ne, kuma mafi ɗaukakar waɗanan aljannatan ita ce aljannar Firdausi, daga nan ne ƙoramun aljanna huɗu suke ɓuɓugowa, a saman Firdausi ne al’Arshi yake; idan zaku roƙi Allah to ku roƙe Shi Firdaus; saboda ita ce a saman dukkaninl aljannatan.

Fassara: Indonisiyanci Vietnam Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Fifikon 'yan aljanna a matsayinsu, hakan kuma gwargwadan imani da ayyuka na gari.
  2. Kwaɗaitarwa akan roƙon Allah Firdausi maɗaukakiya daga gidajan aljanna.
  3. Firdausi ita ce mafi ɗaukakar gidajan aljanna, kuma mafificinsu.
  4. Yana kamata ga musulmi himmarsa ta zama maɗaukakiya, kuma ya yi ƙoƙari ya nemi mafi ɗaukakar matsayai kuma mafifitansu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  5. Ƙoramun aljanna huɗu su ne ƙoramun ruwa da nono da giya da zuma waɗanda aka ambata a ciki AlƘur'ani a cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -; {Kwatankwacin aljannar da aka yi wa masu tsoron Allah alƙawari a cikinta akwai ƙoramu na ruwa ba mai sakewa ba, da ƙoramu na nonon da ɗanɗanonsa bai canja ba, da ƙoramu na giya masu ɗaɗi ga masu sha da ƙoramai na tatacciyar zuma} [Muhammad: 15].