+ -

عَنْ أَبِي بَرْزَةَ الأَسْلَمِيِّ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَزُولُ قَدَمَا عَبْدٍ يَوْمَ القِيَامَةِ حَتَّى يُسْأَلَ عَنْ عُمُرِهِ فِيمَا أَفْنَاهُ، وَعَنْ عِلْمِهِ فِيمَ فَعَلَ، وَعَنْ مَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَ أَنْفَقَهُ، وَعَنْ جِسْمِهِ فِيمَ أَبْلَاهُ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2417]
المزيــد ...

Daga Abu Burzata Al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce :
"Diga-digan bawa ba za su gusheba a ranar Alkiyama har sai an tambaye shi game da rayuwarsa a me ya karar da ita, da kuma iliminsa me ya aikata da shi, da dukiyarsa daga ina ya samota kuma a me ya ciyar da ita, da jikinsa wanne aiki ya yi da shi".

[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2417]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani mutum daga mutane da zai ketare matsayar hisabi a ranar Alkiyama zuwa aljanna ko wuta ba har sai an tambaye shi game da wasu al'amura:
Na daya: Rayuwarsa a me ya karar da ita?
Na biyu: Iliminsa shin ya neme shi ne saboda Allah? kuma ya yi aiki da shi? kuma shin ya isar da shi ga wanda ya cancance shi?
Na uku: Dukiyarsa daga ina ya samota shin daga halal ne ko daga haram? kuma a me ya ciyar da ita a abinda zai yardar da Allah ne, ko a abinda zai fusatar da Shi?
Na hudu: Jikinsa da karfinsa da lafiyarsa da samartakarsa a me ya yi da shi ya kuma aiwatar da shi?

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan ribar rayuwa a cikin abinda zai yardar da Allah - Madaukakin sarki -.
  2. Ni'imomin Allah ga bayinSa masu yawa ne kuma za'a tambaye shi daga ni'imar da ya kasance a cikinta, to ya wajaba akansa ya sanya ni'imomin Allah a abinda zai yardar da Shi.