عَنِ البَرَاءِ بْنِ عَازِبٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«المُسْلِمُ إِذَا سُئِلَ فِي القَبْرِ: يَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ»، فَذَلِكَ قَوْلُهُ: {يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا بِالقَوْلِ الثَّابِتِ فِي الحَيَاةِ الدُّنْيَا وَفِي الآخِرَةِ} [إبراهيم: 27].
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4699]
المزيــد ...
Daga Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4699]
Za'a tambayi mumini a cikin ƙabari, sai mala'iku biyu waɗanda aka wakilta da hakan su tambaye shi su ne Munkar da Nakir, kamar yadda ambatansu ya zo a Hadisai masu yawa, sai ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: wannan shi ne tabbatacciyar magana wacce Allah Ya faɗa a cikinta: {Allah Yana tabbatar da wadanda su ka yi imani da magana matabbaciya a rayuwar duniya da kuma a lahira} [Ibrahim: 27].