عَنْ مُعَاوِيَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«الْمُؤَذِّنُونَ أَطْوَلُ النَّاسِ أَعْنَاقًا يَوْمَ الْقِيَامَةِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 387]
المزيــد ...

Daga Mu'awiya -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Ladanai sune mafiya tsawon wuyaye a ranar alƙiyama".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [Sahih Muslim - 387]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa ladanai waɗanda suke kiran sallah sune mafiya tsawon wuyaye a cikin mutane ranar alƙiyama, saboda girman aikinsu, da kuma yawan alherinsu, da girman ladansu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar kiran sallah da kwaɗaitarwa a cikinsa.
  2. Bayanin matsayin ladanai da ɗaukakar matsayinsu a ranar alƙiyama.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (35)