1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)?

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أَتَدْرُونَ مَا الْمُفْلِسُ؟» قَالُوا: الْمُفْلِسُ فِينَا مَنْ لَا دِرْهَمَ لَهُ وَلَا مَتَاعَ، فَقَالَ: «إِنَّ الْمُفْلِسَ مِنْ أُمَّتِي يَأْتِي يَوْمَ الْقِيَامَةِ بِصَلَاةٍ وَصِيَامٍ وَزَكَاةٍ، وَيَأْتِي قَدْ شَتَمَ هَذَا، وَقَذَفَ هَذَا، وَأَكَلَ مَالَ هَذَا، وَسَفَكَ دَمَ هَذَا، وَضَرَبَ هَذَا، فَيُعْطَى هَذَا مِنْ حَسَنَاتِهِ، وَهَذَا مِنْ حَسَنَاتِهِ، فَإِنْ فَنِيَتْ حَسَنَاتُهُ قَبْلَ أَنْ يُقْضَى مَا عَلَيْهِ أُخِذَ مِنْ خَطَايَاهُمْ فَطُرِحَتْ عَلَيْهِ، ثُمَّ طُرِحَ فِي النَّارِ».

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai ya ce: "Lallai cewa muflis daga al'ummata zai zo ranar alƙiyama da sallah da azumi da zakka, zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, kuma ya yi wa wannan ƙazafi, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya daki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan ayyukansa, wannan ma daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukansa sun ƙare kafin a biya abin ke kansa sai a ɗauka daga kurakuransa sai a watsa masa, sannan a watsa shi a cikin wuta".

Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi Sahih Muslim - 2581

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kun san waye muflis? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dukiya ko kaya, sai ya ce: Lallai muflis daga al'ummata zai zo ranar lahira da ayyuka na gari na sallah da azumi da zakka. Kuma zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, ya yi wa wannan ƙazafi a mutuncinsa, kuma ya ci dukiyar wannan ya yi musunta, kuma ya zubar da jinin wannan ya zalinci shi, ya daki wannan ya wulaƙantashi, sai a bawa wanda aka zalinta daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukan suka ƙare kafin ya biya abinda ke kansa na haƙƙoƙi da abubuwan da aka zalinta, sai a ɗauki zunuban wanda aka zalinta sai a sanya su a takardun azzalimin, sannan a watsa masa sai a jefa shi a cikin wuta inda babu wani kyakkyawan aiki da zai rage gare shi .

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Tsoratarwa ga afkawa a cikin abubuwan da aka haramta, musamman ma abinda ke rataye da haƙƙoƙin bayi na dukiya da na ma'ana.
  2. Haƙƙoƙin mutane a tsakaninsu an gina su ne akan jayayya, haƙƙoƙin Mahalicci kuwa in banda shirka ababen ginawane akan afuwa.
  3. Anfani da hanyar muhawara wacce zata sawa mai ji shauƙi kuma ta juyo da tunaninsa kuma ta motsa himmarsa, musamman ma dai a cikin tarbiyya da fadakarwa.
  4. Bayanin ma'anar muflis na haƙiƙa, shi ne wanda waɗanda suke binsa bashi suka ɗauki ayyukansa na gari a ranar lahira.
  5. Sakayya a lahira za ta iya zuwa a kan dukkanin kyawawan ayyuka, har sai ya zama ba zai rage wani abu ba daga cikinsu.
  6. Mu'amalar Allah ga halitta mai tsayuwace akan adalci da gaskiya.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
BN বাংলা البنغالية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية