عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ اللهَ إِذَا أَحَبَّ عَبْدًا دَعَا جِبْرِيلَ فَقَالَ: إِنِّي أُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبَّهُ، قَالَ: فَيُحِبُّهُ جِبْرِيلُ، ثُمَّ يُنَادِي فِي السَّمَاءِ فَيَقُولُ: إِنَّ اللهَ يُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبُّوهُ، فَيُحِبُّهُ أَهْلُ السَّمَاءِ، قَالَ ثُمَّ يُوضَعُ لَهُ الْقَبُولُ فِي الْأَرْضِ، وَإِذَا أَبْغَضَ عَبْدًا دَعَا جِبْرِيلَ فَيَقُولُ: إِنِّي أُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضْهُ، قَالَ فَيُبْغِضُهُ جِبْرِيلُ، ثُمَّ يُنَادِي فِي أَهْلِ السَّمَاءِ إِنَّ اللهَ يُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضُوهُ، قَالَ: فَيُبْغِضُونَهُ، ثُمَّ تُوضَعُ لَهُ الْبَغْضَاءُ فِي الْأَرْضِ».
[صحيح] - [صحيح مسلم] - [صحيح مسلم: 2637]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi, sannan ya yi kira a cikin sama sai ya ce: Lallai Allah Ya na son wane to kuso shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa.
Idan kuma Ya ƙi wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce; Lallai Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, ya ce sai (Mala’ika) Jibril ya ƙi shi, sannan sai ya yi kira a cikin waɗanda ke cikin sama lallai cewa Allah Yana ƙin wane to ku ƙishi, ya ce: Sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini a cikin ƙasa».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2637]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta cewa Allah idan Ya so bawanSa mumini; mai biyayya ga umarninSa mai nisantar hane-hanenSa sai Ya kira (Mala’ika) Jibril: Lallai cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana son wane to ka so shi. Sai shugaban mala'iku (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya so shi, sai Jibril yayi kira a cikin mala'ikun sama: Lallai cewa Ubangijinku Yana son wane to ku so shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin zukatan muminai da soyayya da kuma karkata gare shi da kuma yarda da shi. Idan Allah Ya ki wani bawanSa sai Ya kira Jibril: Lallai cewa Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, sai (Mala’ika) Jibril ya ƙishi, sannan Jibril yayi kira a cikin waɗanda ke cikin sama: Lallai Ubangijinku Yana ƙin wane to ku ƙishi; sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini da ƙiyayya a cikin zukatan muminai.