عن أبي مسعود رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«إِذَا أَنْفَقَ الرَّجُلُ عَلَى أَهْلِهِ يَحْتَسِبُهَا فَهُوَ لَهُ صَدَقَةٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 55]
المزيــد ...
Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 55]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar matarsa da iyayensa da ‘ya’yansa da sauransu, yana mai neman kusanci zuwaga Allah da hakan, yana neman ladan ciyarwar a wurin Allah, to, Allah zai ba shi ladan sadakarsa.