عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت:
دَخَلَتْ هِنْدٌ بِنْتُ عُتْبَةَ امْرَأَةُ أَبِي سُفْيَانَ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَتْ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ أَبَا سُفْيَانَ رَجُلٌ شَحِيحٌ، لَا يُعْطِينِي مِنَ النَّفَقَةِ مَا يَكْفِينِي وَيَكْفِي بَنِيَّ إِلَّا مَا أَخَذْتُ مِنْ مَالِهِ بِغَيْرِ عِلْمِهِ، فَهَلْ عَلَيَّ فِي ذَلِكَ مِنْ جُنَاحٍ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خُذِي مِنْ مَالِهِ بِالْمَعْرُوفِ مَا يَكْفِيكِ وَيَكْفِي بَنِيكِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1714]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Hindu 'yar Utbatah - matar Abu Sufyan- ta shigo wajen Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ta ce:
Ya Manzon Allah, Abu Sufyan ya kasance mutum ne mai ƙwauro, ba ya bamu abin da zai ishe mu ni da 'ya'ya na sai abinda na ɗauka daga cikin dukiyarsa ba tare da saninsa ba, shin ba laifi akaina a yin hakan? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ki ɗauki abin da zai ishe ki ke da 'ya'yanki daga cikin dukiyarsa ba tare da barna ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1714]
Hindu 'yar Utbah - Allah Ya yarda da ita - ta nemi fatawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mijinta Abu Sufyan - Allah Ya yarda da shi -, kuma shi mutum ne marowaci mai kwaɗayin dukiyarsa, ba ya bata abinda zai isheta ya ishi 'ya'yanta na ciyarwa, sai dai in ta ɗauka a ɓoye cikin dukiyarsa alhali shi bai sani ba, shin akwai wani laifi akanta a hakan? Sai (Annabi) - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ki ɗauki gwargwadan abinda aka sani a al'ada cewa shi zai isa cikin dukiyarsa koda ba tare da saninsa ba.