عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ السَّاعِدِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«رِبَاطُ يَوْمٍ فِي سَبِيلِ اللَّهِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَمَوْضِعُ سَوْطِ أَحَدِكُمْ مِنَ الجَنَّةِ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا، وَالرَّوْحَةُ يَرُوحُهَا العَبْدُ فِي سَبِيلِ اللَّهِ أَوِ الغَدْوَةُ خَيْرٌ مِنَ الدُّنْيَا وَمَا عَلَيْهَا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2892]
المزيــد ...
Daga Sahl ɗan Sa'ad al-sa'idi - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Zaman dakon yini ɗaya saboda Allah shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, kuma bigiren bulalar ɗayanku a aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta, yammacin da bawa zai yi shi saboda Allah ko jijjifi shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke kanta".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2892]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa lazimtar gurin da yake tsakanin musulmai da kafirai dan gadin musulmai daga gare su a yini ɗaya yana mai tsarkake niyya saboda Allah, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma bigiren bulalar da zai yi yaƙi da ita saboda Allah a cikin aljanna shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta, kuma lallai cewa lada da sakamakon tafiya a cikin lokaci daga farkon yini zuwa farkon lokacin azahar, ko yammaci: Daga lokacin azahar zuwa dare saboda Allah sau ɗaya, shi ne mafi alheri daga duniya da abinda ke cikinta.