عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه قَالَ:
سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الرَّجُلِ يُقَاتِلُ شَجَاعَةً، وَيُقَاتِلُ حَمِيَّةً، وَيُقَاتِلُ رِيَاءً، أَيُّ ذَلِكَ فِي سَبِيلِ اللهِ؟ فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ قَاتَلَ لِتَكُونَ كَلِمَةُ اللهِ هِيَ الْعُلْيَا، فَهُوَ فِي سَبِيلِ اللهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1904]
المزيــد ...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mutumin da yake yaƙi dan jarumta, (da wanda) yake yaƙi dan ƙabilanci, (da wanda) yake yaƙi dan riya, wanne ne saboda Allah? sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1904]
An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga saɓanin manufofin masu yin yaƙi; wanda ya yi yaƙi dan jarumtaka ko ƙabilanci ko dan aga matsayinsa a cikin mutane ko wanin hakan, wannene saboda Allah? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa wanda ya yi yaƙi saboda Allah shi ne: Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama ita ce maɗaukakiya.