عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضيَ اللهُ عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا جَمَعَ اللهُ الْأَوَّلِينَ وَالْآخِرِينَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرْفَعُ لِكُلِّ غَادِرٍ لِوَاءٌ، فَقِيلَ: هَذِهِ غَدْرَةُ فُلَانِ بْنِ فُلَانٍ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1735]
المزيــد ...
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan Allah Ya tara mutanen farko da na ƙarshe ranar alƙiyama za'a ɗaga tuta ta dukkan wani mayaufdari, sai a ce: Wannan yaudarar wane ɗan wane ce".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1735]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya tara mutanen farko dana ƙarshe ranar alƙiyama saboda hisabi, za'a kafawa kowanne maha'incin da bai cika alƙawarin da ya dauka ba tare da Allah ko tare da mutane ba, wata alamar da za'a kunya shi da ita akan ha'incinsa, kuma za’a yi kira akan sa a wannan ranar: Wannan ha'incin wane ɗan wane ne; dan bayyanar da mummunan aikinsa a filin taron alƙiyama.