عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُما:
أَنَّ امْرَأَةً وُجِدَتْ فِي بَعْضِ مَغَازِي النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَقْتُولَةً، فَأَنْكَرَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَتْلَ النِّسَاءِ وَالصِّبْيَانِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3014]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3014]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wata mace an kashe ta a ɗaya daga cikin yake-yake, sai ya yi inkarin kashe mata da kananan yara waɗanda basu isa mafarki ba.