عنْ ابنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ:
كُنَّا مَعَ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَانْطَلَقَ لِحَاجَتِهِ، فَرَأَيْنَا حُمَّرَةً مَعَهَا فَرْخَانِ، فَأَخَذْنَا فَرْخَيْهَا، فَجَاءَتِ الْحُمَرَةُ فَجَعَلَتْ تَفْرِشُ، فَجَاءَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «مَنْ فَجَعَ هَذِهِ بِوَلَدِهَا؟ رُدُّوا وَلَدَهَا إِلَيْهَا»، وَرَأَى قَرْيَةَ نَمْلٍ قَدْ حَرَّقْنَاهَا، فَقَالَ: «مَنْ حَرَّقَ هَذِهِ؟» قُلْنَا: نَحْنُ. قَالَ: «إِنَّهُ لَا يَنْبَغِي أَنْ يُعَذِّبَ بِالنَّارِ إِلَّا رَبُّ النَّارِ».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 2675]
المزيــد ...
Daga Ibu Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce:
Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin tafiya, sai ya tafi wata buƙatarsa, sai muka ga wata tsuntsuwa tare da 'yayanta biyu, sai muka ɗauke su, sai tsuntsuwar ta zo tana fakan-fakan (tana nemansu), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «Waye ya raba wannan da ɗanta? ku maida mata da ɗanta», kuma sai ya ga wasu ramin tururuwa wanda muka ƙona shi, sai ya ce: «Waye ya ƙona wannan?» mukace: Mune. Ya ce: «Babu wanda yake yin azaba da wuta sai Ubangijin wuta».
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 2675]
Abdullahi Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa su sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tafi dan wata buƙatarsa, sai sahabbansa suka samu wata tsuntsuwa tare da 'ya'yanta biyu, sai suka ɗaukesu, sai tsuntsuwar ta fara fakan-fakan da fukafukanta tana buɗesu dan firgicin rasa 'ya'yanta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma ya ce: Waye ya baƙanta mata rai ya tsoratar da ita ta hanyar ɗauke mata 'ya'yanta?! Sannan ya yi umarni a mayar mata da su. Sannan ya ga wani ramin tururuwar da aka ƙona shi da wuta, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Waye ya ƙona wannan? Wasu daga cikin sahabbansa suka ce: Mu ne. Sai ya ce da su: Lallai ba ya halatta ga wani ya azabtar da mai rai da wuta; sai Allah Mahaliccinta.