عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَت: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«تُقْطَعُ اليَدُ فِي رُبُعِ دِينَارٍ فَصَاعِدًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6789]
المزيــد ...
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Ana yanke hannu a rubu'un dinari (ɗaya bisa huɗu) zuwa sama".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6789]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ɓarawo ana yanke hannunsa saboda satar rubu'in dinari na zinare, da abinda ya ƙaru a kan hakan, kuma ya yi daidai da abinda ƙimarsa ta yi daidai da ƙimar 1.06 Gram na zinari.