عن عَائِشَةُ رضي الله عنها «أَنَّ قُرَيْشا أَهَمَّهُم شَأن المَخْزُومِيَّة التي سَرَقَتْ، فَقَالُوا: مَنْ يُكَلِّمُ فيها رسول الله صلى الله عليه وسلم ؟، فقالوا: وَمَنْ يَجْتَرِئُ عليه إلا أسامة بن زيد حِبُّ رسول الله صلى الله عليه وسلم فَكَلَّمَهُ أسامة، فَقَالَ: أَتَشْفَعُ فِي حَدٍّ مِنْ حُدُودِ الله؟ ثُمَّ قَامَ فَاخْتَطَبَ، فقال: إنَّمَا أَهْلَكَ الذين مِنْ قَبْلِكُمْ أنهم كانوا إذا سرق فيهم الشريف تركوه، وإذا سرق فيهم الضعيف أَقَامُوا عليه الحد، وَأَيْمُ الله: لَوْ أَنَّ فاطمة بنت محمد سَرَقَتْ لَقَطَعْتُ يَدَهَا». وَفِي لَفْظٍ «كانت امرأة تَسْتَعِيرُ المَتَاعَ وَتَجْحَدُهُ، فَأَمَرَ النبي صلى الله عليه وسلم بِقَطْعِ يَدِهَا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Ankarbo daga A'isha-Allah ya yarda da ita-"Cewa Kuraishawa lamarin Almakhzumiyya datai sata ya damesu,sai suka ce:Waye zai yiwa Manzan Allah tshira da amincin Allah su tabbata agareshi maganarta?,sai suka ce:Ba wanda zai iya tararsa sai Usama Dan Zaid Masoyin Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai Usama ya gaya masa,sai yace:ka nemi Ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah?sannan ya tashi yayi huduba,sai yace:Hakika abinda ya halakar da wadanda suke gabaninku cewa su sun kasance idan wani Mai'alfarma daga cikinsu yayi sata sai su rabu dashi,idan kuma Mairauni ne acikinsu yayi sata sai su tsayar da Hukunci akansa,na rantse da Allah:da cewa Fadima yar Muhammad za tayi sata da lallai na yanke Hannunta".Awata ruwayar kuma"Wata Mace ta kasance tana arar kaya sai kuma ta musashi,sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi umarni da a yanke Hannunta"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Wata Mace daga Bani Makhzum ta kasance tana arar kaya daga wajan Mutane da Zamba,sannan ta musashi.Sai wani lokaci ta ari abin ado ta musashi,sai aka sameshi a wajanta,sai lamarinta ya isarwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai ya nufi zartar mata da Hukuncin Allah Madaukakin Sarki na yanke Hannuwanta,kuma ta kasance Ma'abociyar Alfarma ce,kuma daga Nasaba ta Asali cikin Kuraishu.Sai Kuraishu suka damu da ita da kuma wannan Hukuncin da aka zartar mata,sai sukayi Shawara game da wanda zasu sanya shi Wasida zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi don yai masa magana ya rabu da ita,basu ga wanda yafi Usama Dan Zaidu ba,domin cewa shi Makusancine Abin so ne ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi.Sai Usama ya gaya masa.Sai yayi Fushi dashi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sannan yace dashi-yana mai inkari agareshi-"ka nemi ceto cikin Hukunci daga Hukunce-Hukuncen Allah"?Sannan ya mike don yayi ma Mutane Huduba ya bayyana musu hadarin misalin wannan ceton wanda zai wofuntar da Hukuncin Allah,kuma saboda maubu'in ya dami da yawa daga cikinsu,sai ya basu Labari cewa sababin halakar wadanda suka zo gabaninmu a cikin Addininsu da Duniyarsu:cewa su suna tsaida Hukunci akan Raunana da Fakirai,sai su dinga barin Karfafa da Mawadata,sai Bala'i ya game acikinsu Sharri da Fasadi suka watsu,sai Fushin Allah da Ukubarsa ta cancancesu.Sannan sai ya rantse tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-kuma shi mai Gaskiyane abin gasgatawa-da cewa wannan aiki zai faru akan Shugabar Matan Talikai Yarsa Fadima-Allah ya tsareta da hakan-da sai ya zartarda Hukuncin Allah Madaukaki agareta.Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin