+ -

عن عَبْدُ الله بن عمر رضي الله عنهما أن عمر قال -على منبر رسول الله- صلى الله عليه وسلم : "أما بعد، أيها الناس، إنه نزل تحريم الخمر وهي من خمسة: مِنَ العنب، والتمر، والعسل، والحنطة، والشعير. والخمر: مَا خَامَرَ العَقْلَ. ثَلاثٌ وَدِدْتُ أَنَّ رَسُولَ الله صلى الله عليه وسلم كَانَ عَهِدَ إلَيْنَا فِيهَا عَهْداً نَنْتَهِي إلَيْهِ: الجَدُّ، والكَلالَةُ، وأَبْوَابٌ مِنَ الرِّبَا".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda da su- cewa Umar ya ce:- yana kan minbarin Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi:" Bayan haka, ya ku mutane,tabbas hukuncin haramta giya ya sauka alhaliana yin ta ce daga abubuwa biyar: Inibi,da Zuma,da Alkama da Sha'ir; bin da ake cewa giya: Shi ne duk abin da zai gusar da hankali
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya yi huduba a masallaci Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi- kuma akan minbarinsa, kuma ya tabbatar da cewa lallai giya itaa ce duk wani abu da zai iya jirkita hankali, ba wacce aka yi da inibi ba kawai, duk wani abin sha wanda zai iyi jirkita hankali ko da kuwa da dabino ko zuma ko alkama to suma sun zama giya, kuma hakika Uma r ya fadi abubuwa uku a cikin Hudubarsa wanda akawai rikitarwa a cikinsa kuma yayi burin ace Annabi yana raye, cikim wadan nan abubuwa guda uka da ya da aka kure matuka izuwa gare shi sune Gadon Kaka, da Gadon Mamacin da bashi da Da ko Mahaifi, da wasu abubuwa kan Riba, kuma Alhamdulillah cewa lallai Hukuncin wannan abubuwa guda uku sananne ne, kuma wannan ba yana nufin cewa Annabi baiyi bayaninsu ba Hakika Annabi ya Isar da Sakonsa, kuma ya bada Amana, kuma ya isar da sakon Allah abun da yafi wannan ma buya da kuma wanda ya fi wannan ma girma kuma Umar yana son yakasance akawai nassi gwari gwari ne a kansu da baya bukatar wani Ijtihadi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin