عبدُ الله بنُ عمر رضي اللهُ عنهما «أَنَّ النَّبِي صلى الله عليه وسلم قَطَع فِي مِجَنٍّ قِيمَتُهُ -وَفِي لَفْظٍ: ثَمَنُهُ- ثَلاثَةُ دَرَاهِمَ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An rawaito daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- "Cewa Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yanke Hannu akan wani Silke kimarsa Dirhami Uku"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Allah Madaukaki ya tsare jinin mutane da mutuncinsu da dukiyoyinsu, da duk wani abu da zai tunkude masu barna masu ketare iyaka.sai Allah ya sanya yanke hannun da yake da shi ake yin sata ya zama ukubar wanda ya dauki dukiyar da take a boye;don yanke hannun ya zame masa kankarar zunubinsa, kuma don shi wanda yayi satar da wani ma wanda ba shi ba suyi nesa da aikata hakan,su tafi neman na kansu ta hanyar da shari'a ta yarda da ita,sai aiki ya yawaita, sai a sami sakamakon hakn,kasa ta ginu rayuka su daukaka, yana daga hikimar Allah Madaukaki,sanya dan adadi karami a matsayin abin da za'a yanke hannu in aka dauke shi,dayan hudun zinare daya,don kare dukiyoyi,da tsare rayuwa.don tsaro ya tabbata,zukata su nutsu,mutane su yada dukiyoyinsu don tsuwuri da neman karuwar arziki.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Kurdawa Portuguese Malayalam
Manufofin Fassarorin