+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«قَالَ اللهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ أُنْفِقْ عَلَيْكَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5352]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5352]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da ta Mustahabbi zan yalwata maka, zan kuma ba ka makwafin abin da ka bayar, kuma in sanya maka albarka.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa a kan sadaka da kuma ciyarwa Fi-sabilillahi.
  2. Ciyarwa ta ɓangarorin alheri yana daga cikin manyan dalilan samun albarka a arziki da kuma ninka shi, da kuma yadda Allah zai mayarwa bawa abin da ya ciyar.
  3. Wannan hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaitoshi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai cewa shi babu keɓance-keɓancen Alkur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karantashi, da yin tsarki sabo da shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, da sauransu.