عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «ما نقصت صدقة من مال، وما زاد الله عبدا بعفو إلا عزا، وما تواضع أحد لله إلا رفعه الله عز وجل »
[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Wannan fassarar tana bukatar Karin bita da gyaran yare.

An karbo daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- cewa Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Babu wata Dukiya da ta taba tawaya saboda Sadaka, Kuma wani abu da Allah yake Karawa Bawa da Rangwame sai Daukaka, kuma babu wani daya da zai Kaskantar da kansa ga Allah face Allah Madaukakin sarki ya daukaka shi."
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]

Bayani

(Dukiya bata taba tawaya ba don anyi Sadaka) Lallai cewa Sadaka idan aka futar da ita to cewa ita ba zata tawaya ba aa karuwa ma zatayi, kuma Albarka ta shiga cikinta, kuma akawutar da asara daga ita, kuma karuwar arziki tana iya Kasancewa kodai ta hanyar Yawa: Kamar Allah yayi budi ga Bawa na arziki, ko kuma ta Hanyar Samun kamar Allah ya saukar masa da Albarka wacce zata kara Masa yawan abunda ya futar na Sadaka, kuma Allah bai taba karar bawa da Afuwa ba face sai ya daukaka shi; ai duk wanda aka sanshi da Afuwa da barin ramuwa ko Korafi, to zai Girma kuma a zujata kuma zai jagoranci, zai kara girma da Daukaka, da Daraja a Duniya da Lahira, kuma Mutum bai taba kaskantar da kai ba face sai Allah ya daga Darajarsa, Ma'ana duk wanda ya Kaskantar da kansa ga Allah, kuma ya risina gare shi, kuma ya kasance mai saukin kai ga Mutane, kuma ya nuna Taushinsa ga Musulmai, domin wadan Siffofi ba zasu Karawa Maisu komai ba sai daukaka a Duniya da kuma Soyayya a Zukata, da Matsayi Babba a cikin Al-janna.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu
Manufofin Fassarorin