+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا جَلَسَ قَوْمٌ مَجْلِسًا لَمْ يَذْكُرُوا اللَّهَ فِيهِ وَلَمْ يُصَلُّوا عَلَى نَبِيِّهِمْ إِلاَّ كَانَ عَلَيْهِمْ تِرَةً، فَإِنْ شَاءَ عَذَّبَهُمْ وَإِنْ شَاءَ غَفَرَ لَهُمْ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى] - [سنن الترمذي: 3380]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu".

[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3380]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga rafkana daga ambatan Allah, kuma cewa wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba kuma basu ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai wannan mazaunin ya zama hasara a kansu da nadama da taɓewa da tawaya a ranar alƙiyama, idan Ya so Ya azabtar da su saboda zunubinsu da ya gabata da kuma kasawarsu mai zuwa, idan kuma Ya so Ya gafarta musu dan falala da rahama daga gare shi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tamili Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗaitarwa akan zikiri da kuma falalarsa.
  2. Falalar wuraran zama da a cikinsu akwai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, da ambatan ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma cewa majalisan da a cikinsu babu hakan to sune majalisan zargi ga ma'abotansu a ranar alƙiyama.
  3. Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa ba ne akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin ba tare da ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  4. Hasara mai faruwa ce garesu a ranar Alkiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin a saɓon Allah.
  5. Wannan gargaɗin idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba da annamimanci da wasunsu?!