عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَا مِنْ يَوْمٍ يُصْبِحُ العِبَادُ فِيهِ إِلَّا مَلَكَانِ يَنْزِلاَنِ، فَيَقُولُ أَحَدُهُمَا: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُنْفِقًا خَلَفًا، وَيَقُولُ الآخَرُ: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُمْسِكًا تَلَفًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1442]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1442]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa:
Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka.
Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.