عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه:
أَنَّ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالُوا لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: يَا رَسُولَ اللهِ، ذَهَبَ أَهْلُ الدُّثُورِ بِالْأُجُورِ، يُصَلُّونَ كَمَا نُصَلِّي، وَيَصُومُونَ كَمَا نَصُومُ، وَيَتَصَدَّقُونَ بِفُضُولِ أَمْوَالِهِمْ، قَالَ: «أَوَلَيْسَ قَدْ جَعَلَ اللهُ لَكُمْ مَا تَصَّدَّقُونَ؟ إِنَّ بِكُلِّ تَسْبِيحَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَكْبِيرَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَحْمِيدَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَهْلِيلَةٍ صَدَقَةً، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ صَدَقَةٌ، وَنَهْيٌ عَنْ مُنْكَرٍ صَدَقَةٌ، وَفِي بُضْعِ أَحَدِكُمْ صَدَقَةٌ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَيَأتِي أَحَدُنَا شَهْوَتَهُ وَيَكُونُ لَهُ فِيهَا أَجْرٌ؟ قَالَ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ وَضَعَهَا فِي حَرَامٍ أَكَانَ عَلَيْهِ فِيهَا وِزْرٌ؟ فَكَذَلِكَ إِذَا وَضَعَهَا فِي الْحَلَالِ كَانَ لَهُ أَجْرٌ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1006]
المزيــد ...
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi -
Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: "Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne", Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1006]
Wasu daga talakawan sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku: Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.