عَنْ أَبي مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ مِمَّا أَدْرَكَ النَّاسُ مِنْ كَلاَمِ النُّبُوَّةِ الأُولَى: إِذَا لَمْ تَسْتَحْيِ فَاصْنَعْ مَا شِئْتَ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6120]
المزيــد ...
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6120]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa daga abinda ya zo a cikinsa wasicci game da Annabawa magabata, kuma mutane suka jujjuya shi tsakaninsu kuma suka gaje shi daga garesu ƙarni bayan ƙarni, har sai da yakai zuwa farkon wannan al'ummar, ka duba zuwa abinda kake son ka aikata shi, idan ya kasance abinda ba'a jin kunyarsa ne to ka aikata shi, idan ya kasance daga abinda ake jin kunyarsa ne to ka bar shi; domin abinda yake hana munanan ayyuka shi ne kunya, wanda ba shi da kunya, to sai ya kutsa a cikin kowace alfasha da abin ƙi.