عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ وَهُوَ عَلَى المِنْبَرِ، وَذَكَرَ الصَّدَقَةَ، وَالتَّعَفُّفَ، وَالمَسْأَلَةَ: «اليَدُ العُلْيَا خَيْرٌ مِنَ اليَدِ السُّفْلَى، فَاليَدُ العُلْيَا: هِيَ المُنْفِقَةُ، وَالسُّفْلَى: هِيَ السَّائِلَةُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1429]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce akan minbari, kuma sai ya ambaci sadaka, da kamewa, da kuma roƙo: «Hannu maɗaukaki shi yafi alheri daga hannu maƙasƙanci, hannu maɗaukaki: Shi ne mai ciyarwa (mai bayarwa) maƙasƙanci kuma: Shi ne mai roƙo».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1429]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambata alahali yana huɗubar akan sadaka da kamewa daga roƙo akan minbari; sannan ya ce: Hannau maɗaukaki mai ciyarwa mai bayarwa shi ne nafi alheri kuma mafi soyuwa a wurin Allah daga hannu maƙasƙanci mai roƙo.