lis din Hadisai

Naji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kafin mutuwarsa da (darare) biyar alhali shi yana cewa: "@Lallai ni ina barranta zuwa ga Allah da ya zama ina da badadi daga cikinku, to lallai cewa Allah - Madaukakin sarki - hakika Ya rike ni badadi, kamar yadda Ya riki (Annabi) Ibrahim badadi*, da na kasance mai rikon badadi daga al'ummata da na riki Abubakar badadi, ku saurara lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna maida kaburburan Annabawansu da salihansu masallatai, ku saurara kada ku maida kaburbura masallatai, lallai ni ina hanaku hakan".
عربي Turanci urdu
Wata rana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsaya a cikinmu, sai ya yi mana wa'azi, wa'azi isasshe zukata suka ji tsoro daga gare shi, idanuwa suka zubar da hawaye daga gareshi, aka ce: Ya Manzon Allah ka yi mana wa'azin bankwana to ka yi mana alkawari. Sai ya ce: '@Na horeku da tsoron Allah, da ji da bi, koda bawa ne mutumin Habasha, za ku ga sabani mai tsanani a bayana, to na horeku da sunnata da sunnar Halifofina shiryayyu*, ku rike su da turamen hakoranku, na haneku da fararrun al'amura, domin cewa kowacce bidi'a bata ce".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa"* Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: Ban so shugabanci ba sai wannan ranar, ya ce sai na yi ɗigirgire saboda ita dan kwaɗayin a kirawoni gareta, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira Aliyu bin Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ba shi ita, ya ce: "Ka tafi, kada ka juya, har sai Allah Ya buɗe maka." Ya ce sai Aliyu ya tafi ɗan wani taku, sannan ya tsaya bai juya ba, sai ya yi magana: Ya Manzon Allah, akan me zan yaƙi mutane? Ya ce: "Ka yaƙesu har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, idan suka aikta hakan to hakika sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai da hakkinsu kuma hisabinsu yana ga Allah".
عربي Turanci urdu
"Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa".
عربي Turanci urdu
"Duk mutumin da ya halarci (yaƙin) Badar da Hudaibiyya ba zai shiga wuta ba".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Ku wuce Abubakar, ku bar shi ya yi Sallah tare da mutane
عربي Turanci urdu
Shin bana jin kunyar mutumin da yake jin kunyar mala'iku
عربي Turanci urdu
Wannan ne wanda Al'arshi ya girgiza saboda shi, kuma aka buxe masa kofofin Sama, kuma Mala'iku Dubu Saba'in suka raka shi, haqiqa an mastse Matsewa, sannan aka sake shi
عربي Turanci urdu
Ya Ubangiji ka gafartawa Mutanen Madina da "Ya'yan Mutanen Madina, da 'Ya'yan Mutanen Madina
عربي Turanci urdu
Lallai kowace Alumma tana da Amintaccen ta, kuma lallai amintaccen wannan Al-umma shi ne Abu Ubaidah Bn Al-Jarrah
عربي Turanci urdu
Ban taba ganin wani mutum da ya Manzon Allah SAW ya fansheshi ba bayan Sa'ad naji shi yana cewa: Ka harba fansarka da Mahaifana
عربي Turanci urdu
Ya Ubangiji kasanya shi Shiyayye kuma maishiryarwa kuma ka shiryar da shi
عربي Turanci urdu
Ya Amirul Muminina, Allah Madaukaki ya ce wa Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Ka yi afuwa ka yi umarni da al'ada kuma ka kau da kai daga jahilai.
عربي Turanci urdu
Haqiqa a Hannuna Takubba Tara sun karye a ranar yaqin Mu'ata, babu abunda ya ragu a Hannuna sai Takobin Yamani
عربي Turanci urdu
Abu Jumah Al-Ansari ya zo mana, sai ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Moaz bin Jabal yana tare da mu goma, sai muka ce: Ya Rasulallahi, shin akwai wanda ya fi mu lada mai girma?
عربي Turanci Fassara Yaren Faransanci
Lallai Allah ya sanya Gaskiya a kan Harshen Umar da zuciyarsa
عربي Turanci Fassara Yaren Faransanci
Naga Ja'afar yana tashi tare da Mala'iku a cikin Al-janna
عربي Turanci Sifaniyanci
Manzon Allah SAW ya Kasance yana sany da Silke ranar Uhudu, sai yayi zunbur zuwa wani dutse, bai iya hawa ba, sai ya zaunar da Xalha aqarqashinsa, sai ya hau SAW kansa, har saida ya daidaita akansa, sai ya ce: naji Mazon Allah SAw yana cewa ta Wajaba ga Xalha.
عربي Turanci urdu
Sa'ad ya zo sai Manzon Allah SAW ya ce: Wannan Kawu na ne kowane Mutum ya nuna mun kawunsa
عربي Turanci urdu
B'a tava bawa Ammar zavin abubuwa biyu sai ya zavi mafi dacewarsu
عربي Turanci Sifaniyanci
Ya'yan Al-as Muminai ne Amr da Hisham
عربي Turanci Sifaniyanci
Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: @ Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
عربي Turanci urdu
«Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu»* Imran ya ce: Ban sani ba shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agatre shi - bayan nan ya ambaci ƙarni biyu ne ko uku, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai a bayanku za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'iinci ba'a amince musu ba, sunayin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba, suna bakance ba sa cikawa, kuma ƙiba zata bayyana a cikinsu».
عربي Turanci Indonisiyanci