+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ يَوْمَ خَيْبَرَ:
«لَأُعْطِيَنَّ هَذِهِ الرَّايَةَ رَجُلًا يُحِبُّ اللهَ وَرَسُولَهُ، يَفْتَحُ اللهُ عَلَى يَدَيْهِ» قَالَ عُمَرُ بْنُ الْخَطَّابِ: مَا أَحْبَبْتُ الْإِمَارَةَ إِلَّا يَوْمَئِذٍ، قَالَ فَتَسَاوَرْتُ لَهَا رَجَاءَ أَنْ أُدْعَى لَهَا، قَالَ فَدَعَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلِيَّ بْنَ أَبِي طَالِبٍ، فَأَعْطَاهُ إِيَّاهَا، وَقَالَ: «امْشِ، وَلَا تَلْتَفِتْ، حَتَّى يَفْتَحَ اللهُ عَلَيْكَ» قَالَ فَسَارَ عَلِيٌّ شَيْئًا ثُمَّ وَقَفَ وَلَمْ يَلْتَفِتْ، فَصَرَخَ: يَا رَسُولَ اللهِ، عَلَى مَاذَا أُقَاتِلُ النَّاسَ؟ قَالَ: «قَاتِلْهُمْ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، فَإِذَا فَعَلُوا ذَلِكَ فَقَدْ مَنَعُوا مِنْكَ دِمَاءَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ، إِلَّا بِحَقِّهَا وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللهِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2405]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya faɗa a ranar Khaibara:
"Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa" Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: Ban so shugabanci ba sai wannan ranar, ya ce sai na yi ɗigirgire saboda ita dan kwaɗayin a kirawoni gareta, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira Aliyu bin Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ba shi ita, ya ce: "Ka tafi, kada ka juya, har sai Allah Ya buɗe maka." Ya ce sai Aliyu ya tafi ɗan wani taku, sannan ya tsaya bai juya ba, sai ya yi magana: Ya Manzon Allah, akan me zan yaƙi mutane? Ya ce: "Ka yaƙesu har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, idan suka aikta hakan to hakika sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai da hakkinsu kuma hisabinsu yana ga Allah".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2405]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bada labarin samun nasarar musulmai a gobe akan Yahudawan Khaibara wani gari ne kusa da Madina, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta, shi ne wata alama wacce runduna suke riƙonta dan alama gareta, wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da ManzonSa, kuma Allah da ManzonSa suna sonsa.
Hakika Uamr ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa shi bai taɓa son shugabanci ba kuma ya zama shi ne abin nufi sai a wannan ranar; dan kwaɗayin abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗe shi na son Allah da ManzonSa ya same shi , kuma Umar - Allah Ya yarda da shi ya daga kansa dan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi dan kwaɗayin a kira shi gareta, da kuma kwaɗayi a karɓar waccan tutar.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kira Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - sai ya bashi tutar, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarce shi ya tafi da rundunar, kuma kada ya juya baya a yaƙi bayan haɗuwa da maƙiya dan hutu ko tsayawa ko sulhu har sai Allah Ya buɗe masa waɗannan katangun da nasara da kuma rinjaye.
Sai Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya tafi, sannan ya tsaya sai dai bai juya ba; dan kada ya saɓa umarnin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai Ali - Allah Ya yarda da shi - ya ɗaga muryarsa: Ya Manzon Allah, akan me zan yaki mutane?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka yaƙesu har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, idan sun amsa, sun shiga Musulunci; to haƙiƙa sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareka kuma sun haramta daga gareka, sai dai da haƙƙinsu, yana nufin sai dai idan sun aikata laifi ko jinayar da zasu cancanci kisa akansu da wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية النيبالية الرومانية Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sahabbai sun kasance suna ƙin shugabanci dan abinda ke cikinsa na nauyi mai girman gaske.
  2. Halaccin mike wuya da dagowa dan wani al'amarin da alherinsa yake da ƙarfi.
  3. Fadakarwar shugaba ga jagoran runduna a yanayin tasarrufi a fagen yaƙi.
  4. Lazimtuwar sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wasiyyoyinsa da kuma gaggawa ga zartar da su.
  5. Wanda wani abu ya rikitar da shi a cikin abinda aka neme shi da shi to ya yi tambaya game da shi.
  6. Daga dalilan Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labarinsa da nasara akan Yahudawa, inda ya bada labari game da buɗe Khaibara sai ya zama kamar yanda ya bada labarin.
  7. Kwaɗaitarwa akan fuskanta da gaggawa zuwa abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da shi.
  8. Ba ya halatta kashe wanda ya furta kalmar shahada biyu sai dai idan abinda yake wajabta kisa ya bayyana daga gare shi.
  9. Hukunce-hukuncen Musulunci suna gudana ne akan abinda yake bayyana daga mutane Allah kuma Yana jiɓintar abinda suka ɓoye.
  10. Abin nufi mafi girma daga yaƙi shi ne shigar mutane cikin Musulunci.