عن أنس رضي الله عنه، قال:
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لأبي بكر وعمر: «هذان سَيِّدا كُهُول أهل الجنة من الأوَّلِين والآخِرين إلا النبيِّين والمرسلين».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 3664]
المزيــد ...

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni".

[Ingantacce ne] - [Tirmizi ne ya ruwaito shi] - [Sunan Tirmizi - 3664]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Abubakar Siddiƙ da Umar Faruƙ - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa, kuma mafifitan waɗanda suka shiga aljanna bayan Annabwa da Manzanni.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa da Manzanni.
  2. A aljanna babu tsoho, kai, wanda zai shigeta ɗan shekara talatin da uku ne, abin nufi cewa sune shugabannin wanda ya mutu yana dattijo a duniya, ko kuma hakan izina ne na abinda suke akansa a duniya a lokacin wannan hadisin.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Indonisiyanci Kari (44)