عَنْ ‌أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ افْتَقَدَ ثَابِتَ بْنَ قَيْسٍ، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَعْلَمُ لَكَ عِلْمَهُ، فَأَتَاهُ فَوَجَدَهُ جَالِسًا فِي بَيْتِهِ، مُنَكِّسًا رَأْسَهُ، فَقَالَ: مَا شَأْنُكَ؟ فَقَالَ شَرٌّ، كَانَ يَرْفَعُ صَوْتَهُ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَدْ حَبِطَ عَمَلُهُ، وَهُوَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ، فَأَتَى الرَّجُلُ فَأَخْبَرَهُ أَنَّهُ قَالَ كَذَا وَكَذَا، فَرَجَعَ الْمَرَّةَ الْآخِرَةَ بِبِشَارَةٍ عَظِيمَةٍ، فَقَالَ: «اذْهَبْ إِلَيْهِ فَقُلْ لَهُ: إِنَّكَ لَسْتَ مِنْ أَهْلِ النَّارِ، وَلَكِنْ مِنْ أَهْلِ الْجَنَّةِ».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi
Lallai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nemiSabitu ɗan Ƙais (domin bai ganshi ba) sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan samo maka labarinsa, sai ya zo masa sai ya same shi a zaune a gidansa ya sunkuyar da kansa, sai ya ce: Meke damunka? sai ya ce: Sharri, ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to, haƙiƙa aikinsa ya ɓaci, kuma shi yana daga 'yan wuta. Sai mutumin ya zo sai ya ba shi labarin cewa kaza da kaza, sai ya dawo a karo na ƙarshe da babban albishir, sai ya ce: "Ka tafi zuwa gareshi ka ce masa: Lallai kai ba ka cikin 'yan wuta, sai dai kana daga cikin 'yan aljanna".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya rasa Sabitu Dan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - ya yi tambaya game da shi (ya yi cigiyarsa), sai wani mutum ya ce: Ni zan samo maka labarinsa, da dalilin fakuwarsa, sai ya tafi wurinsa sai ya same shi yana cikin baƙin ciki yana mai sunkuyar da kansa a gidansa, sai ya tambaye shi : Meke damunka? sai Sabitu ya ba shi labarin abin da ke tare da shi na sharri; domin cewa ya kasance yana ɗaga sautinsa sama da sautin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma haƙiƙa Allah Ya yi alkawarin narko daga aikata hakan da ɓacin aikinsa, kuma cewa shi yana daga 'yan wuta!
Sai mutumin ya dawo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sanar da shi da hakan, sai Annabi - tsaira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce shi ya koma wa Sabitu ɗan Ƙais ya yi masa albishir da cewa shi ba ya daga 'yan wuta, sai dai yana daga 'yan aljanna, domin cewa ya kasance mai babbar murya ne a halitta, domin shi ya kasance mai huɗubar Manzon Allah ne - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. kuma mai yi wa mutanen Madina huɗuba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar Sabitu ɗan Ƙais - Allah Ya yarda da shi - kuma cewa shi yana daga cikin 'yan aljanna.
  2. Damuwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbai da bibiyarsa garesu.
  3. Tsoron sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da ɓacin aikinsu.
  4. Wajabcin ladabi wajen yi masa magana - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a rayuwarsa, da ƙanƙan da muryoyi a lokacin jin sunnarsa bayan ya rasu.