عن أنس بن مالك رضي الله عنه مرفوعًا: «إنَّ لكل أُمَّة أمِينًا، وإنَّ أمِيننا -أيتُها الأمة- أبو عُبيدة بن الجَرَّاح».  
                        
[صحيح] - [متفق عليه]
                        
 المزيــد ... 
                    
An rawaito daga Anas Bn Malik -Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah: "Lallai kowace Alumma tana da Amintaccen ta, kuma lallai amintaccen wannan Al-umma shi ne Abu Ubaidah Bn Al-Jarrah" 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]                                            
A cikin kowace Al-umma daga cikin Al-ummai wani Mutum da ya shahara da Amana sama da kowa, kuma mafi Shaharar wannan Al-ummar da Amana shi Abu Ubaidah Amir Bn Al-jarrah -Allah ya yarda da shi- saboda shi koda yake amanar ta kasance sifa ce da kowa daga cikin sahabbai yayi tarayya da shi a cikinta -Amincin Allah ya tabbata a gare su- sai sigar Hadisin tana nuna cewa ya xaresu a cikinta