+ -

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ تَسُبُّوا أَصْحَابِي، فَلَوْ أَنَّ أَحَدَكُمْ أَنْفَقَ مِثْلَ أُحُدٍ ذَهَبًا مَا بَلَغَ مُدَّ أَحَدِهِمْ، وَلاَ نَصِيفَهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3673]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3673]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga zagin sahabbai, musamman ma marigaya na farko daga muhajirai da mutanen Madina; kuma ya bada labarin cewa shi da wani daga mutane zai ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinari ladansa ba zai kai ladan ciyarwar wani daga sahabbai ba mudu na abinci ko rabinsa ba - mudu shi ne cikin tafuka biyu na mutum matsakaicin halitta -; hakan dan ƙarin ikhlasinsu, da gaskiyar niyyarsu, da rigayar ciyarwarsu da yaƙinsu kafin buɗe Makka inda tsananin buƙatuwa gare shi take.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Zagin sahabbai - Allah Ya yarda da su - haramun ne, kuma yana daga manyan zunubai.