عَنْ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّهُ جَاءَ إِلَى الحَجَرِ الأَسْوَدِ فَقَبَّلَهُ، فَقَالَ: إِنِّي أَعْلَمُ أَنَّكَ حَجَرٌ، لاَ تَضُرُّ وَلاَ تَنْفَعُ، وَلَوْلاَ أَنِّي رَأَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقَبِّلُكَ مَا قَبَّلْتُكَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1597]
المزيــد ...
Daga Umar - Allah ya yarda da shi -:
Cewa shi ya zo wurin Hajarul Aswad (Baƙin dutse) sai ya sumbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni naga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1597]
Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya zo wajen Hajarul Aswad a kusurwar Ka'aba sai ya sunbace shi, sai ya ce: Lallai ni nasan cewa kai dutse ne, baka cutarwa kuma baka anfanarwa, da badan cewa ni na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana sunbatarka ba da ban sunbaceka ba.