عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال: ((رَقيت يومًا على بيت حفصة، فرَأَيتُ النبيَّ -صلَّى الله عليه وسلَّم-يَقضِي حاجته مُسْتَقبِل الشام، مُسْتَدبِر الكعبة)).
وفي رواية: ((مُسْتَقبِلا بَيتَ المَقدِس)) .
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda dasu- yace: (Wata rana Na hau saman gidan Hafsa,sai naga Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yana biyan bukatarsa ya fuskanci Sham,ya juyawa Ka'aba baya). A wata ruwayar((ya fuskanci Baitalmakdis)).
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Dan Umar -Allah ya yarda dasu- wata rana yazo gidan 'yar'uwarsa Hafsa,Matar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-sai ya hau saman gidanta, sai ya gano Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yana biyan bukatarsa ya fuskanci Sham,ya kuma juyawa Alkibla baya.Dan Umar Allah ya yarda da shi- ya fadi haka don yin raddi ga wadanda suka ce:Annabi baya fuskantar Baitalmakdis lokacin biyan bukata,daga nan kuma sai Mawallafin ya zo da ruwaya ta biyu wacce take cewa: yana mai fuskantar Baitalmakdis.