عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا يُمْسِكَنَّ أَحَدُكُمْ ذَكَرَهُ بِيَمِينِهِ وَهُوَ يَبُولُ، وَلَا يَتَمَسَّحْ مِنَ الْخَلَاءِ بِيَمِينِهِ، وَلَا يَتَنَفَّسْ فِي الْإِنَاءِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 267]
المزيــد ...
Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 267]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana wasu ladubba; yayin da ya hana mutum ya riƙe azzakarinsa a halin fitsari da hannunsa na dama, ko kuma a gusar da najasa daga gaba ko baya da hannun dama; domin dama an tanadeta ne dan manyan abubuwa, kamar yadda ya yi hani mutum ya yi numfashi a cikin ƙwaryar (kofi) da yake sha acikinta.