+ -

عَنْ عِمْرَانَ بْنِ حُصَيْنٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«خَيْرُكُمْ قَرْنِي، ثُمَّ الَّذِينَ يَلُونَهُمْ، ثُمَّ الَّذِينَ يَلُونَهُمْ» قَالَ عِمْرَانُ: لاَ أَدْرِي أَذَكَرَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بَعْدُ قَرْنَيْنِ أَوْ ثَلاَثَةً، قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ بَعْدَكُمْ قَوْمًا يَخُونُونَ وَلاَ يُؤْتَمَنُونَ، وَيَشْهَدُونَ وَلاَ يُسْتَشْهَدُونَ، وَيَنْذِرُونَ وَلاَ يَفُونَ، وَيَظْهَرُ فِيهِمُ السِّمَنُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2651]
المزيــد ...

Daga Imran ɗan Hussain - Allah - Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Mafi alherinku zamanina, sannan waɗanda suke biye musu, sannan waɗanda suke biye musu» Imran ya ce: Ban sani ba shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agatre shi - bayan nan ya ambaci ƙarni biyu ne ko uku, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai a bayanku za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'iinci ba'a amince musu ba, sunayin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba, suna bakance ba sa cikawa, kuma ƙiba zata bayyana a cikinsu».

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2651]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin ɗabaƙa ta mutane masu taruwa a zamani ɗaya sune ɗabaƙar sahabban da a cikinsa akwai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa, sannan waɗanda suke biye musu cikin muminan da suka riski sahabbai amma ba su riski Manzon Allah ba, sannan waɗanda suke biye musu sune masu biyewa tabi'ai, sahabin ya yi kaikawo a cikin ambatan waɗanda suke biye musu ga ƙarni na huɗu. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai a bayansu za'a samu wasu mutane zasu dinga ha'inci, mutane ba za su amince da su ba, kuma zasu dinga yin shaida kafin a nemi shaida daga garesu, zasu yi bakance ba sa cikawa, zasu dinga yalwatawa a ciye-ciye da abubuwan sha har sai ƙiba ta bayyana a cikinsu.

Fassara: Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mafi alherin ƙarni da jama'a a dukkan shekarun duniya shi ne ƙarnin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rayu a cikinsa da sahabbansa, haƙiƙa ya zo a cikin Sahihul Bukhari daga gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya ce: "An aikoni daga mafi alherin zamaninnikan Banu Adam ƙarni sai ƙarni, har na zama daga ƙarnin da nake a cikinsa".
  2. Ibnu Hajar ya ce: Wannan hadisin ya hukunta cewa sahabbai su zama sun fi tabi'ai, tabai'ai kuma sun fi waɗanda ke binsu, sai dai wannan fifikon shin dangane da tattaron jama'a ne ko ɗaiɗaiku? Wannan abu ne na bincike, amma ra'ayi na biyun (ɗaiɗaiku) shi ne wanda jumhur ɗin malamai suka tafi akai.
  3. Nuni zuwa lazimtar bin hanyar zamaninnika uku na farko; domin cewa wanda zamaninsa ya kusanci zamanin Annabta to shi ya fi falala da ilimi da koyi da shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  4. Bakance: Shi ne mukallafi ya lazimtawa kansa wani aikin ɗa'ar da Mai Shari’a ba ta lazimta masa ba ta hanyar maganar da take nuni a kansa.
  5. Zargin ha'inci da rashin cika alƙawari da rataya da duniya.
  6. Zargin shaida ba tare da an nemi shaidarsu ba idan mai haƙƙin yana sanin hakan, idan ya kasance ba shi da sanin hakan sai ya shiga cikin faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Shin bana baku labari ba da mafi alherin masu shaida shi ne wanda yake zuwa da shaidarsa kafin a tambaye shi ita» Muslim ne ya ruwaito shi .