+ -

عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كَانَتْ عَامَّةُ وَصِيَّةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حِينَ حَضَرَهُ الْمَوْتُ: «الصَّلَاةَ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ، الصَّلَاةَ وَمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ»، حَتَّى جَعَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُغَرْغِرُ بِهَا صَدْرُهُ، وَمَا يَكَادُ يُفِيضُ بِهَا لِسَانُهُ.

[صحيح] - [رواه النسائي في السنن الكبرى وابن ماجه] - [مسند أحمد: 12169]
المزيــد ...

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce:
Wasiyyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai gamewa ta kasance lokacin da rasuwarsa ta zo masa: «Ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka, ku kula da sallah da abinda hannayenku suka mallaka», har Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara gargarar mutuwa, amma harshensa bai iya faɗinta ba.

[Ingantacce ne] - - [مسند أحمد - 12169]

Bayani

Mafi yawan wasiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa ta kasance alhali shi yana cikin magagin mutuwa: Ku lazimci sallah ku kiyayeta, kada ku rafkana daga gareta, haka nan haƙƙoƙin abinda hannayenku suka mallaka na bayi maza da kuyangi mata ku kyautata mallakinsu, bai gushe ba yana maimaita ta, har maƙogwaransa ya fara gargarar mutuwa da ita, harshensa bai kusa ya bayyananar da ita ba.

Fassara: Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Girman sha'anin sallah da haƙƙin abinda hannu ya mallaka; domin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wasicci da su a cikin ƙarshen abinda ya yi wasicci (da shi).
  2. Sallah tana daga mafi girman haƙƙin Allah akan bayinSa, da kuma bada haƙƙin halitta musamman ma raunana da waɗanda suke ƙarƙashin hannu waɗanda ba iyalai ba yana daga mafi girman haƙƙoƙin halitta.