+ -

عن عائشة رضي الله عنها قالت: ((دخل عبد الرحمن بن أبي بكر الصديق رضي الله عنهما على النبي صلى الله عليه وسلم وأنا مُسْنِدَتُه إلى صدري، ومع عبد الرحمن سِواك رَطْب يَسْتَنُّ به، فأَبَدَّه رسول الله صلى الله عليه وسلم بَصَره، فَأَخَذْتُ السِّوَاك فَقَضَمتُه، فَطَيَّبتُه، ثُمَّ دَفَعتُهُ إلى النبي صلى الله عليه وسلم فَاسْتَنَّ به فما رأيتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم استَنَّ اسْتِنَانًا أَحسَنَ منه، فَما عَدَا أن فَرَغَ رسول الله صلى الله عليه وسلم : رَفَع يَدَه -أو إصبعه-، ثم قال: في الرفيق الأعلى -ثلاثا- ثمَّ قَضَى، وكَانت تقول: مَاتَ بَينَ حَاقِنَتِي وَذَاقِنَتِي)).
[صحيح] - [رواه البخاري]
المزيــد ...

Daga Aisha Allah ya yarda da ita- tace: ((Abdurrahman Dan Abubakar Assiddik -Allah ya yarda dasu ya shiga wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, a lokacin Na jingina Annabi a kirji na, A wajen Abdurrahman akwai danyen asuwaki, sai Manzo tsira da amincin Allah ya kalli asuwakin, sai Na karbi asuwakin Na tauna masa shi, Na kuma kansasa shi, sannan Na baiwa Annabi tsira da aminci yayi asuwakin da shi, ban taba ganin Manzon Allah ya yi asuwaki mai kyau irn wannan ba, yana gamawa sai ya daga hannunsa ko danyatsansa sannan yace: Izuwa abota madaukakiya sau uku sannnan ya rasu. Aisha ta kasance tana fadar cewa: ya rasu a tsakanin haba ta da cinyoyi na)).
Ingantacce ne - Buhari ne ya rawaito shi

Bayani

Aisha tana bada labarin irin kaunar da Annabi tsira da amincin Allah ke yiwa asuwaki da kuma yadda ya damu da shi. Shi ne take fadar yadda Dan'uwanta - Allah ya yarda da shi- ya zo da danyen asuwaki wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi lokacin barinsa duniyan. lokacin da Annabi tsira da aminci yaga asuwakin a wajensa, rashin lafiyarsa bata hana shi nuna yana son asuwakin ba, sai ya kalli asuwakin, kamar yana so, sai Aisha Allah ya yarda da ita ta kula da haka sai ta karbi asuwakin daga hannun Dan'uwanta ta sa bakinta ta gyarawa Annabi asuwakin, ta bashi ya goge bakinsa da shi -tsira da aminci su tabbata a gare shi. Aisha bata taba ganin wanda ya fi shi iya goge baki ba. Bayan ya gama goge bakin, sai ya daga yatsansa sama, yana dayanta Allah Madaukaki, sannan ya zabi komawa kusa da Mahaliccinsa, sannan ya rasu. Aisha tav kasance cikin farin ciki, ya cancanta tayi farin ciki kuwa, don kuwa Manzo tsira da amincin Allah ya rasu kansa na jingine a kirjinta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin