kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Abdurrahman Dan Abubakar Assiddik -Allah ya yarda dasu ya shiga wajen Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, a lokacin Na jingina Annabi a kirji na, A wajen Abdurrahman akwai danyen asuwaki, sai Manzo tsira da amincin Allah ya kalli asuwakin
عربي Turanci urdu
An karvi ran Manzon Allah SAW kansa yana tsakanin Wuyana da Qirjina, yayin da ransa ya futa, ban tava jin wani qanshi kamar wannan
عربي Turanci urdu
Qarshen ganin da nayiwa Manzon Allah SAW shi ne lokacin da ya buxe labule yaga Mutane sunyi Sahu a bayan Abubakar -Allah ya yarda da shi
عربي Turanci urdu
Ku wuce Abubakar, ku bar shi ya yi Sallah tare da mutane
عربي Turanci urdu
Bana kishin Mutuwar wani da Mutuwa da tafi bani tsoro da tsanani kamar Mutuwar Manzon Allah SAW
عربي Turanci urdu
Yayin da Annabi SAW ya rasu sai suka ce: a ina za'a Binne shi? sai Abiubakar ya ce: a wurin da ya ra su a cikinsa
عربي Turanci urdu
Cewa Abubakar ya shiga ga Annabi SAW bayan Wafatinsa, sai ya sanya bakinsa akan Idanunsa, ya sanya Hannayensa akan Mukamukinsa, kuma ya ce: "Ya Annabi, ya Badadi, ya zababbe"
عربي Turanci urdu
Yayin da Manzon Allah SAW ya shiga Madina a cikinta kowane abu ya haskaka, kuma Ranar da ya rasu a cikinta kowane abu a cikinta yayi duhu
عربي Turanci urdu
Ba'a rabawa Magadana ko dinare daya ko Dirhami abunda na bari bayan abincin Iyalina, da ladan Ma'aikata na to sauran Sadaka ne
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW bai bar Dinare da Dirhami ba ko Akuya ko Raqumi kuma bai yi Wasiyya da komai ba
عربي Turanci urdu
Lallai ba'a karvar ran wani Annabi face sai an nuna masa Masaukinsa a Al-janna, sannan a bashi zavi" to yayin da Mutuwa ta sauka gare shi, Kansa yana kan cinyata sai ya suma, sannan ya farka sai idonsa ya kafe yana kallon rufin xakin, sannan ya ce: "Ya Ubangiji kusanci Mafi xaukaka"
عربي Turanci urdu
Ya Allah, ka gafarta mini ka yi mani rahama, kuma ka riskar da ni da mafi girman abokin zama
عربي Turanci urdu
Yayin da ya Wanke Manzon Allah SAW ya tafi yana neman abunda ake samu ga Mamaci, bai samu komai ba, sai ya ce: Fansarka da Mahaifina , Kana tsaftace a halin kana da Rai, haka ma bayan ka Mutu
عربي Turanci Uighur